Gwamnan Jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya halarci bikin ƙaddamar da sabon shugaban Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labaru na Ƙasa—BON Mr. John Ugbe da mataimakin sa Dr. Mansur Liman.
Taron bikin ya wakana a ranar Asabar a ɗakin taro na Transcorp Hilton, Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: A yankin Arewa kaɗai muke so kuyi amfani da Jiragen Super Tucano — Cewar Amurka ga Najeriya
Dayake jawabi a lokacin taron, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa Shugabar Hukumar Kafafen Yaɗa Labaru-BON Hajiya Sa’a Ibrahim, tare da taya murna ga sabbin Shuwagabannin Hukumar, inda suka bada tabbacin yin aiki tuƙuru.
Gwamnan ya samu rakiyar Sanata Kabiru Gaya, da Daraktan gangamin yaƙin zaɓen shi Alhaji Nasiru Aliko Ƙoki, da tsohon Mataimakin Gwamnan Jahar Kano Abdullahi Tijjani Gwarzo, da Kwamishinan Yaɗa Labaru Kwamared Muhammad Garba.
Sauran sun haɗa da; Shugaban Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labaru ta Ƙasa, kuma Shugabar gidan Talabijin na ARTV Hajiya Sa’a Ibrahim, da Mai ba Gwamna Shawara na Musamman akan ayyuka na musamman Muhammad Zakari da sauran su.