By Ishaq Dabai
A yau ne Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya mika ragamar rikon mulkin Kano na tsawon awa daya ga wata yarinya mai shekara sha hudu mai suna Atika Aminu Yankaba.
Gwamnan ya mika mulkin ne yayin da ake gudanar da bikin ranar ‘ya’ya mata ta duniya wacce majalisar dinkin duniya ta ware duk ranar sha daya ga watan Oktoba na kowace shekara.
Atika ta karbi mulkin ne da misalin karfe shabiyu na rana zuwa karfe daya na rana inda daga nan ne ta sake mika ragamar mulkin ga Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Taron ya samu halartar Sakataren Gwamnatin kano Alhaji Usman Alhaji da Kwamishinan Yada labarai, kwamared Muhammad Garba, da shugabar gidan talabijin na gwamnatin jihar kano ARTV, Hajiya Sa’a Ibrahim da Arch. Aminu Dabo da sauran jami’an Gwamnati.