Gwamnati jihar kano ta yi alkawarin sake samar da jami’o’i guda 2 a Kano domin Kara bada damar inganta Ilimin matasa a jihar.
Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi, yayin bude taron makon matasa wanda Majalisar dinkin duniya ta ware domin duba kan matsalolin matasa da Kuma lalubo hanyoyin da za’a magancesu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa taron a gudanar da shi ne rufaffen dakin taro na filin wasa na Sani Abacha dake unguwar kofar mata.
KARANTA ANAN: Sojoji Sun Hallaka Yan Ta’addan Boko Haram 6 A Wani Luguden Wuta Da Su Kayi
Gwamna Ganduje yace tuni an tura sunayen kwalejin horar da malamai ta sa’adatu Rimi da Kuma kwalejin koyar da aikin noma ta Audu Bako dake Danbatta ga hukumar da take kula da jami’o’i ta kasa (NUC) domin neman sahalewa.
Gwamnan Ganduje ya ce yayi hakan ne domin Kara baiwa matasa damar su Kara karatu, don inganta Rayuwarsu da Kuma cigaban jihar kano baki daya.
Idan wadannan jami’o’i suka tabbata Kano tana da jami’o’i guda 4 kenan mallakin gwamnatin jiha.
A wani labarin kuma;
Yadda Turkiyya Ta Tilastawa Yan Wasan Najeriya Kwana A Filin Jirgi