Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya zabtare Kashi hamsin cikin dari na albashin masu rike da mukaman Siyasar Jihar a watan Maris.
Wannan mataki na zuwa ne kwana guda bayan da Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin ba za ta iya biyan albashin watan Maris ga Ma’aikatan Jihar baki daya ba, sakamakon abin da ta kira da rashin samun cikakken kudin tallafi da aka saba samu daga gwamnatin tarayya.
Cikin wadanda wannan zabtare albashi ya shafa, akwai shi kan sa gwamnan jihar da mataimakin sada dukkanin kwamishinoni da manyan mashawartan shi babban mai tallafa mishi gami da manyan masu tallafa mishi.
Sauran sun haɗa da Shugabannin Ƙananan Hukumomi da mataimakan su da Kansiloli da masu bada shawara gami da dukkanin sakatarorin kananan hukumomin jihar.
A wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar Muhammad Garba ya fitar ya ce an dauki wannan mataki ne sakamakon ƙarancin kudaden shiga da gwamnatin ke samu daga asusun gwamnatin tarayya.
To sai dai Ƙungiyar kwadagon jihar ta baiwa gwamnatin wa’adin mako guda da ta gaggauta maido da kuɗaɗen da ta zabtare, wanda a cewar ba ya bisa ka’ida.