Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya halarci taron addu’o’i na musamman da aka shirya domin dawowar zaman lafiya da tsaro a jihar da ma Najeriya baki.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa taron addu’o’in ya gudana ne a garin Ilorin na jihar Kwara.
Darakta Janar ga Gwamnan bangare Sabbin Kafafan yada labarai, Al-Amin Isa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai yau Laraba a Katsina.
Wike Yana Da Cikakkiyar Damar Ganawa Da Duk Wanda Ya So – Ologbondiyan
“Dr Abdulraheem Oladimeji, wanda ya kafa Jami’ar Al-Hikima, a Ilorin ne ya shirya taron addu’ar domin rokon Allah kan zaman lafiya a Katsina da Najeriya baki daya,” in ji Isa.
A cewarsa, taron addu’ar ya gudana ne karkashin jagorancin babban limamin jami’ar, Dakta Kamaladdeen Al-Mubarak, kuma taron ya samu halartar manyan malaman addinin musulunci daga sassan kasar nan.
Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa babban abin da ya fi daukar hankali a taron shi ne kaddamar da wani masaukin dalibai mata mai sunan Gwamnan.