Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya amince da nadin sabbin alkalai takwas a ma’aikatar shari’a ta jihar, Daily Post ta rawaito.
Nadin ya biyo bayan shawarar da hukumar shari’a ta kasa ta bayar ne a taronta na 100 da ta gudanar a ranar 18 ga watan Junairu, 2023 kuma bisa tanadin sashe na 271 karamin sashe (2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 kamar yadda aka yi wa kwaskwarima
KARANTA WANNAN LABARIN: Tabarbarewar Kudi: Emefiele Yana Yakar Rashin Samun Nasarar Takararsa Ta Shugaban Kasa Ne – Ganduje
Wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Kunle Somorin ya fitar a ranar Lahadin data gabata a Abeokuta, ta bayyana cewa sabon nadin na alkalan ya dogara ne da girma, kwarewa da kuma aiki.
Wadanda za a rantsar a wani bikin da aka shirya gudanarwa a cibiyar al’adu ta ranar 12 ga watan Yuni dake Abeokuta, a cewar Somorin, sun hada da babban magatakarda na babbar kotun shari’a ta jihar Ogun, Oluwafunke Omolara Odubanjo, Esq; Babban Alkalin Kotun Jihar Ogun, Awofeso Ireti-Olu Babatunde; Mataimakin babban magatakardar babban kotun shari’a na jihar Ogun, Adelaja Adeola Ireti; Babban lauya kuma babban sakatare na ma’aikatar shari’a ta jihar Ogun, Adebayo Bamidele Adedapo da sakataren hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Ogun, Basirat Bolanle Adebowale.
Sauran su ne; Ayodele Adebayo Omoniyi, wani kwararren lauya mai zaman kansa dake Ilaro; Sunday Olufemi Adeniyi, wani kwararren lauya mai zaman kansa da ke Legas da Abimbola Christopher Shokunbi, wani kwararren lauya mai zaman kansa kuma mazaunin Legas.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, nadin na daya daga cikin kokarin da gwamnatin ke yi na sake fasalin tsarin shari’a na jihar domin samun inganci da kuma gudanar da adalci cikin gaggawa a fadin jihar.
A wani labarin kuma,Godiya Ga Al’ummar Igbo Mazauna Kaduna Bisa Kaunar Da Suka Nuna – Uba Sani
Dan takarar gwamna a jihar Kaduna na jam’iyyar APC kuma Sanata mai ci Sanata Uba Sani ya yabawa yan kabilar Igbo mazauna jihar.
Sanata Uba Sani ya yabawa al’ummar Igbo mazauna Kaduna ya yi wani taron nuna masa goyan bayansu gare shi da takarar da yake yi.