By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara a ranar Laraba ya gabatar da kiyasin kasafin kudi na Naira biliyan 189.4 a gaban majalisar dokokin jihar na shekarar 2022.
Abdulrazaq wanda ya sanya wa kasafin lakabin “Kasafin Kuɗi mai Dorewar Gyara don Ci Gaba” yace ya kasance ya fi kashi 12.5 fiye da girman kasafin kudin shekarar 2021 da aka yi wa kwaskwarima.
A cewarsa, yawan kudin da za’a kashe ya kai kashi 55.3% na (Naira biliyan 101) yayin da kashi 44.7% ya kai (Naira 84.7bn) a matsayin kudaden da za’a kashe akai-akai ya kara da cewa zai mai da hankali ne a kan kammala ayyukan da ake ci gaba da yin sa da kuma fara sabbi a cikin sabuwar shekarar.
Sannan yace “Girman tsarin kasafin kudin ya kai Naira biliyan 189.4bn wanda ke nuna karin kashi 12.15% akan kasafin kudin shekarar 2021 da aka yi wa kwaskwarima.
Kazalika yace “Yana da kashi 44.7% na maimaituwa, tare da tanade-tanaden biyan bashin daya biyo baya na mafi karancin albashi.
“Tare da kaso 55.3% na kudaden da za’a kashe wanda makasudin shine don tallafawa ayyukan dake gudana da kuma ƙaddamar da sababbi kamar yadda albarkatun ke ba da izini.