Gwamnan Jahar Nasarawa Abdullahi Sule ya kira taron tsaro na gaggawa kan kisan Deborah Samuel, inda yayi gargaɗi kan gudanar da zanga-zanga a Jahar.
Gwamnan ya kuma yi Allah Wadai da kisan Ɗalibar, inda ya bayyana haka a matsayin rashin girmama Ɗan Adam.
Sule a jawabin shi na buɗe taro a gidan Gwamnatin Jahar dake Lafia yace Gwamnatin Jahar Sokoto data Tarayya na ɗaukar matakai domin magance matsalar.
Gwamnan yace Gwamnatin sa ta ɗauki matakai domin kiyaye Al’umma tare da tabbatar dacewa irin haka bai wakana ba a Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Nasarawa ya kora taron tsaro na Gaggawa, yayi Allah Wadai da Kashe Deborah
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan bindiga sun kashe mutane 6, sun sace Dagaci a Kano
Gwamnan yace dalilan daya sanya ya kira taron, shine domin jajantawa Iyalan Deborah Samuel, Kiristoci da Al’umma baki ɗaya.
Yayi kira ga Shuwagabannin Ƙungiyar Kiristoci a Jahar da kada su shirya zanga-zanga, sakamakon yanayin da Jahar Nasarawa take ciki, da kuma tsoron cewa Tsageru na iya karɓe zanga-zangar.
Comments 1