By Ishaq Dabai
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce manufar hana kiwo a fili da wasu takwarorinsa na kudancin kasar nan suka dauka ba ta aiki a jihar sa, gwamnonin Enugu, Ribas, Akwa Ibom, Ondo da Legas duk sun sanya hannu kan dokar hana kiwo a sarari.
Wannan ya biyo bayan kudurin da aka cimma a taron Kungiyar Gwamnonin Kudu, inda gwamnonin kudancin suka tsayar da ranar 1 ga Satumba, 2021, a matsayin ranar da za a sanya hannu kan dokar.
A wata hira da yayi a gidan talabijin na Channels, Sule ya ce ya yi imanin shirin baya aiki, “Ba mu son manufar hana kiwo sa fili a yanzu, ba ta aiki,” in ji shi
Duk da haka, Sule ya ce ya yi imanin cewa rayuwar makiyaya ba ita ce hanyar da za a bi ba, “Abu daya da dukkan gwamnonin arewa suka yanke, mun ce hanyar da ake bi yanzu na kiwo a bude ta tsufa, ba ta da amfani, kuma ba za a iya dorewa ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa a madadin dokar hana kiwo a fili, Nasarawa ta yanke shawarar amincewa da Tsarin Canjin Dabbobi na Kasa.Ya yi bayanin cewa gwamnatinsa ta yi shirin sasanta makiyaya ta hanyar kafa wuraren kiwo a wurare bakwai a cikin jihar, matakin daya dace an dauki shi tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya da Gwamnatin Netherlands.
“Hanya mafi kyau don yin hakan ita ce idan kuna da zaɓuɓɓuka don mutane, abu ne mai sauki Nasarawa tace cikin mako guda, za muje Majalisar don ci gaba da samun dokar hana kiwo.”
“To me zai faru da Fulanin da ke kai da kawowa? Idan Fulanin sun san dalilin da yasa baya aiki, hanya mafi kyau shine a basu wani abu mai aiki, ”inji shi.