An yi wani abu mai kama da wasan kwaikwayo a majalisar dokokin jihar Neja a yau Alhamis yayin gabatar da kasafin kudin 2022.
Gwamna Abubakar Sani-Bello ya isa a zauren Majalisar a makare domin gabatar da kasafin a harabar majalisar, inda ya jinkirta gudanar da aikin kasafin na sama da mintuna 25.
Kakakin majalisar Abdullahi Bawa Wuse ya shiga zauren majalisar ne da misalin karfe 10:30 na safe bayan an yi addu’ar bude taron zaman majalisar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Anambra: Dillalan Man Fetur zasu dakatar da kasuwancin su a yau
An karanta zaman na ranar tare da gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 da gwamna ya gabatar a matsayin babban abin da ya kamata.
A lokacin da aka bukaci shugaban masu rinjaye, Sale Ibrahim mai wakiltar mazabar Kontagora ya shigar da Sani Bello cikin zauren majalisar domin gabatar da kiyasin kasafin kudin, sai aka sanar da shugaban majalisar har yanzu bai je harabar majalisar ba.
Kakakin majalisar ya yi gaggawar ba da uzurin rashin halartar taron, inda ya ce “’Yan uwa Gwamna yana kan hanyarsa ta zuwa Majalisa, za mu jira sai ya zo kafin mu fara. Ina tabbatar muku cewa yana dab da karasowa Majalisar kuma nan ba da jimawa ba zai zo nan.”
Duk da wannan tabbacin, sai da Gwamnan ya kwashe sama da mintuna 25 kafin ya isa harabar domin gabatar da shi.
Comments 1