Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya kaddamar da kwamitin bincike na mutum takwas da zai binciki kashe-kashen da aka yi a Maza-Kuka, Adogon Malam Kulho da sauran al’ummomin karamar hukumar Mashegu da ke jihar. Mai shari’a Danladi Ahmad ne zai jagoranci kwamitin.
Gwamnan ya ce kashe-kashen da ake yi a wasu Yankuna na jihar ya biyo bayan gazawar gwamnati wajen hukunta masu daukar doka a hannunsu yadda ya kamata.
“Dole ne mu iya yin abin da ya dace. Wadanda suke daukar doka a hannunsu dole ne a gansu su fuskanci shari’a domin a hana wasu aiwatar da irin wadannan ayyukan na rashin hankali da kuma tabbatar da cewa, ba za su sake faruwa a nan gaba ba.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Siyasa Ba zata hanani Harkar Fim Ba
Gwamnan ya dorawa hukumar alhakin yin adalci da gaskiya tare da yin cikakken bincike, yana mai jaddada cewa, ya kamata a gurfanar da wadanda aka samu da laifi a gaban kuliya kamar yadda doka ta tanada.