Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun, a yau Alhamis ya sanya hannu kan dokar hana kiwo a jihar.
A ranar 8 ga watan Yuli ne majalisar dokokin jihar ta zartar da wani kudiri mai taken: “Dokar Kiwon Dabbobi da Dokar Kafe Dabbobi, 2020.”
Kakakin Majalisar, Olakunle Oluomo ya ce, dokar za ta magance rikicin da ba a dade ba tsakanin manoma da makiyaya a jihar.
Ya Kara da cewa, “Kudirin ya tanadi zaman gidan yari na kasa da shekaru uku, ba tare da zabin biyan tara ga duk Wanda aka kama ya karya wannan doka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun farmaki Ayarin Dan Majalissar da ya koma APC jiya a Anambra
“Hakanan ya ba da shawarar a kwace garken shanu ko na dabbobi Kuma a Mika su ga gwamnatin jihar, na duk wanda ya yi kiwo a safari a kowane yanki na jihar, face wuraren da gwamnatin jihar ta amince da su”
Idan za’a iya tunawa, Jihohi da dama a Kudancin kasar ciki har da Ondo da Delta, sun rattaba hannu kan dokar hana kiwo a bainar jama’a.
A wani labarin Kuma na daban.
Sanata mai wakiltar Neja ta gabas Mohammed Sani Musa ya ce, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta nuna ‘rashin tausayi’ a kan ‘yan fashi.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Sanatan na jam’iyyar APC ya fadi haka ne a jiya Laraba, 29 ga watan Satumba, yayin wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels.
Idan na yi magana kan yan bindiga, kawuna za su gwaru, inji Sanata Sani Musa inda Kuma ya ce, ya kamata a tambayi Ahmad Gumi kan yadda yake tuntubar yan bindiga
Yayin da yake amsa tambayoyi kan yadda al’amura suka gudana a mazabarsa da jihar Neja Baki daya, dan majalisar ya ce, jihar ta dan samu zaman lafiya na dan wani lokaci, amma yanzu lamarin ya tsananta.
Ya Kara da cewa, “A cikin watanni shida da suka gabata, abin ya munana. Sai lokacin da sabbin shuwagabannin tsaro suka zo sannan aka dauki wasu mataki, daban da abin da suke yi a da.”
Musa ya ce ya kamata a tambayi Ahmad Gumi, babban malamin addinin Islama wanda ya sha yin magana da yawun ‘yan fashi kan yadda yake tuntubar su.
Kazalika ya ce,”Ina tuna cewa daya daga cikin shahararrun malaman addinin Musulunci, Sheikh Gumi, ya kasance a wani lokaci yana shiga cikin dazuzzuka don kasancewa tare da wadannan mutane.”
“Ina ganin ya kamata a tambayi mutum kamar Gumi yadda yake kira don isa ga waɗannan mutanen. Kuma idan zai iya kai wa ga wadannan mutanen, me yasa bai iya taimakawa gwamnati ba, don ganin an kashe mutanen nan? ”a cewar shi.