Gwamnan Jihar Ogun Dapo Abiodun zai rantsar da shugabannin kananan hukumomi 20 na jihar da mataimakansu.
Da ma dai a ranar Alhamis ne hukumar zabe mai zaman kanta a jihar ta sanar da sakamakon zaben da ya gudana a jihar.
Ana sa ran da tsakar ranar Litinin din ne gwamna Abiodun zai rantsar da shugabannin kananan hukumomin a dakin taro na Arcade Ground dake gidan gwamnatin Jihar kamar yadda Sakataren gwamnatin jihar sanar.