
- Gwamnan Zamfara Matawalle ya dakatar da Zarota
- Mai girman gwamnan jihar ya gaddamar da wani kwamiti da zai bibiyi kundin aikin Zarota.
- Gwamnan ya sanar da dakatar da ƙungiyar Zarota ne a jiya Alhamis bayan jin korafe korafe da yawan waɗanda mutane keyi kansu.
Yakubu Haidara sakataren na dindindin ya bayyana cewar daga yau ƙungiyar Zarota zasu dinga aikine tare da Ƙungiyar ƴan sanda da ƙungiyar masu kula da hanyoyi (Road Safety) da ƙungiyar masu bada kariwa wa al’umma (civil defense).
KARANTA:- An damƙe manyan ƴan bindiga dake Oyo
Mai girman gwamnan jihar ya gaddamar da wani kwamiti da zai bibiyi kundin aikin Zarota.
Yace “duba da haka ana shawartar mutane dasu zama masu bin doka da tsare kansu.
A ranar Alhamis data gabata ne manyan motoci suka rufe hanyar Gusau zuwa Zariya suna bayyana rashin jindadin aikin ƙungiyar.
Abun da ya janyo tsaiko na tafiye tafiyen mutanen garin, gami da ɗaliban makarantar Jami’ar Gusau.
Shugaban masu manyan motoci yace ” sun dauki wannan matakin ne bayan sunta kai koke su kan aikin ƙungiyar amma anyi kunnen uwar shegu da hakan.
Ƙungiyar Zarota dai Mai Girma Gwamna AbduAziz Yari ya kafata domin su kula da zirga zirga akan hanyoyin.
Tun wancan lokacin dai aketa korafi kan irin yadda jagororin ƙungiyar Zarota ke yin yadda suka gadama.
A WANI LABARIN:- Anyankema wata mata Hukuncin watanni shida a gidan kaso bayan banakwa gidan Amaryar tsohon mijinta wuta.sohon mijinta wuta.
Matarmai suna Zainab ibrahim an yanke mata hukuncinne a wata kotun Shari’ar Musulunci dake Rigasa a Kaduna
ZainabIbrahim ta kona gidan Amaryar tsohon Mijinta tare da wasu kayayyakin amfaninta
Alkalin kotun Abubakar-Tureta ya bukaci Zainab da ta biya diyyan kayan data kona nai naira Dubu Dari da Talatin da Daya