Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ce bai bayyana tsabar kudi da jari, da kadarorin Naira tiriliyan 9 ba.
Gwamna Lawal Dare ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake tattaunawa da Rediyon Faransa RFI Hausa.
KU KARANTA: Matsalar Tsaro: Gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani Ya Gana Da Shugabannin Tsaron Jihar
Ya ce al’ummar Zamfara ba za su fuskanci kalubale mai yawa ba idan yana da Naira tiriliyan 9, ya ce da ya yi amfani da kudin wajen ci gaban jihar.
Gwamnan ya ce wannan zargin hasashe ne da mutane ke neman haddasa barna, inda ya ce kadarorinsa na nan ga masu son tantancewa.
”Ina fata haka kuma ina rokon Allah Ya ba ni irin wannan kudin. Allah Ya ba ni irin wannan kudi domin in taimaki jama’ata,” inji shi.
“Idan ina da irin wannan kudi, duk kalubalen da mutanena ke fama da su, da na yi amfani da kudin wajen magance matsalolin.
“Yanzu wannan batu na jama’a ne kuma akwai fom ga wanda yake so ya tabbatar ya zo ya yi nasa binciken.
“Wannan ba komai ba ne illa zargin da ‘yan son yada barna ke yi, masu son ja da sunana amma na gode wa Allah, a kan wannan kudi da suke zargin na ayyana, ina rokon Allah Ya ba ni makudan kudi. don haka zan iya amfani da shi don taimakon jama’ata.”
A wani labarin kuma: An Bukaci Masoyan Lionel Messi Kowa ya Biya Dala 680 Domin Arba Da Shi A China
Magoya bayan kwallon kafa na kasar Sin za su bukaci fitar da kudi har dala 680 don ganin Lionel Messi.
Messi dai shine dan wasan da zai jagoranci Argentina da Australia a wasan sada zumunta na Beijing, in ji masu shirya gasar.
Wasan da za a yi ranar 15 ga watan Yuni a filin wasa na ma’aikata mai daukar mutane 68,000, wasa ne na karawar Argentina da Australia a zagaye na 16 na gasar cin kofin duniya na Qatar.