Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Bello Matawalle ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Manzon Allah (S), inda ya yi kira gare su da su yi amfani da wannan damar wajen gudanar da addu’o’i na musamman wajen dorewar zaman lafiya a jiharsa.
Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Daraktan lura da kafafen watsa labarai na gwamnan, Malam Yusuf Idris ya fitar a ranar Litinin a Gusau.
Gwamnan har wala yau ya ce; lokacin maulidi lokaci ne na murnar tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (S), inda ya ce; ya kamata a yi amfani da wannan lokaci wajen sulhunta rikice-rikice, mutunta juna da kuma yafiya, kamar yadda Annabi (S) ya karantar.
Har wala yau ya ci gaba da cewa; yana amfani da wannan damar wajen kira ga Musulmi da su ci gaba da rayuwa bisa koyarwar Annabi Muhammad wajen nuna gaskiya, adalci, zaman lafiya da kuma soyayya ga kowa, ba tare da nuna bambancin fahimta ba, wanda gwamnan ya ce ya kamata a samu wadannan dabi’u ga dukkanin Musulmi.
Ya yi kira ga Musulmi jihar, da su yi amfani da lokacin Maulidi wajen gudanar da addu’o’in samun dawwamammen zaman lafiya, wanda gwamnan ya ce an samu ne sakamakon sulhuntawa da tattaunawa.
Gwamnan ya ce akwai bukatar al’umma su rungumi zaman lafiya, domin a cewarsa, babu abin da gwamnati za ta iya yiwa al’umma idan babu zaman lafiya.
A karshe, gwamnan ya jaddada manufar gwamnatinsa na bunkasa walwalar jama’ar jihar, ta hanyar kyawawan manufofi da zai shafi al’umma baki daya.