Gwamnan Zamfara Bello Matawallen Maradun ya sha alwashin sanya iyaka ga masu amfani da kafafen sada zumunta wajan yada labarai marasa inganci. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Gwamnan yayi wannan sanarwar ce a wajen gaddamar da Shuwagabannin mata na Yan jaridu mai suna (NAWOJ), a Gusau.
Kwamishinan yada labarai na Jahar Malam Ibrahim Dorasa, shine ya wakilci gwamnan, inda ya kara da cewa za su dauki matakai ga duk wanda aka kama yana cigaba da yada labarai marasa tushe.
KARANTA:- Jirage 30 cikin 60 da aka tantance za su biya haraji, Cewar hukumar Kwastom
Kamar yadda ya bayyana, batagarin Yan siyasa na amfani da kafafen watsa labarai wajan yada labarai marasa inganci domin cimma muradin su a siyasa.
“Yada labarai na karya na daya daga cikin dalilin da ya sanya muka kasa shawo kan matsalar tsaro dake addabar mu.”
“Labarai na karya ya sanya dayawa daga cikin wasu garuruwa basa ganin kimar sojoji da gwamnati.”
“Muna rayuwa a wani karbi mai wahalar sha’ani a kafafen sada zumunta, duk da dai akwai alfanu da yawa tattare da ita, amma kafafen sada zumunta sun zamto madaddalar yada labarai marasa tushe, inda haka na haifar da barazanar zaman lafiya da hadin kan jama’a.” Kamar yadda Matawallen ya bayyana.
Ya cigaba da cewa ” Hakikanin gaskiya gwamnati na na ganin mutuncin Yan jaridu, domin inganta sha’anin mulkin mu, muna da kyakykyawan alaka da kafafen watsa labarai da masu amfani da ita.”
“A koda yaushe muna kokarin ganin mun inganta ra’ayoyin Yan jaridu kamar ku.”
“Za mu cigaba da kulla alaka daku da kafafen sada domin cimma kudirorin mu na ciyar da jahar Zamfara gaba.”
Mataimakiyar shugaban kungiyar ta NAWOJ, Hajiya Halima Musa, ta bayyana farin cikinta bisa yadda gwamantin jahar Zamfara ke kokari akan kafafen sada zumunta, gami da tafiya tare da kungiyar Mata a Jahar.
Tayi alkawarin cewa kungiyar NAWOJ, za ta zama babbar wakiliyar jahar Zamfara a kowane guri.
Shuwagabanni kungiyar sun hada da, Salamatu Abdullahi daga NTA, Rukayya Salahu Sakatariya, Nafisa Kanoma daga gidan Rediyon Zamfara, Shafa’atu Shuaibu, Fatima Dorasa, Nabila Khamis, Farida Abdullahi daga Liberty Tv.