Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayar da hutun kwanaki uku a jihar domin baiwa al’ummar jihar damar kammala yin rijistar zabe kafin wa’adin ranar 31 ga watan Yuli.
Mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Talata.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/yajin-aikin-gargadi-na-kwana-3-za-mu-dora-idan-gwamnatin-tarayya-ta-gaza-daukar-mataki-nlc/
Sanarwar ta bukaci duk wadanda suka cancanci kada kuri’a da su karbe lokacin yin rajista domin su samu damar yin amfani da ‘yancinsu na kada kuri’a.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira ga mazauna jihar da su yi rajista kafin ranar 31 ga watan Yuli, 2022.
“Gwamnatin jihar ta kuma ayyana ranakun 27 zuwa 29 ga watan Yulin 2022 a matsayin ranakun hutun jama’a domin baiwa ‘yan kasa damar kammala yin rijistar zabe.”
Sannan Sanarwar da ta fito daga gidan Sir Kashim Ibrahim ta bukaci daukacin mazauna jihar da su yi amfani da wannan damar domin yin rijistar zabe, don haka su kasance cikin ikon yin amfani da ‘yancinsu na kada kuri’a.
Gwamnati ta bukaci dukkan ma’aikatan da su rika tallafa wa ma’aikatansu don yin rajista kafin hukumar zabe mai zaman kanta ta rufe rajistar masu zabe a ranar 31 ga watan Yuli, 2022.”