Gwamnati a Kano ta sanya dokar hana hawan babur mai ƙafa biyu a wasu ƙananan hukumomi
Ƙananan Hukumomin Gabasawa, Gezawa, Minjibir da Warawa sun dakatar da hawa Babur mai ƙafa biyu daga ranar Lahadi mai zuwa.
Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban karamar hukumar Gezawa Alhaji Hudu Usman Zainawa ya fitar jiya Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kisan Hanifa: An gabatar wa da Kotu kayan shaidar aikata laifi 10 kan Abdulmalik Tanko
Sanarwar ta ce, dokar zata rika aiki daga ƙarfe 11 na dare zuwa 5:30 na asubahin kowacce rana domin kyautata tsarin a yankunan.
Haka zalika sanarwar ta buƙaci Al’ummar ƙananan hukumomin da su bada hadin kai ga jami’an tsaro, domin samun nasarar gudanar da aikin su.
A wani Labarin Kuma
Wata Uwa Da Yaran Ta 3 Sun Kone Kurmus A Jihar Ebonyi
Wata mata da ‘ya’yanta uku sun mutu a wata gobara da ta tashi a Aguabata Echara, karamar hukumar Ikwo ta jihar Ebonyi, kamar yadda hukumar kashe gobara ta jihar ta bayyana.
Daraktan hukumar kashe gobara, Raphael Ibiam, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata yayin da wadanda abin ya shafa suke bacci a gidansu.
“A dalilin tashin gobarar, an shaida mana cewa wani mutum daya wanda ake zargin mazaunin yankin ne ya haddasa gobarar.
“Mun samu labarin cewa mutumin ya kona gidansu da daddare. Gobarar ta kashe wata mata da ‘ya’yanta uku,” inji shi.
Wani dan uwan matar mai suna Samuel Okoro ya yi zargin cewa da gangan ne gobarar ta tashi domin babu wani daji da ya kone a kusa da ginin.