Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce gwamnati da hukumomin tsaro sun gaza wajen tabbatar da tsaron ‘yan Najeriya.
Masari, wanda jiharsa na cikin wadanda suka fi fama da matsalar ‘yan fashi, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa.
Da yake mayar da martani kan matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan, musamman yankin Arewa maso Yamma, Masari ya ce, “Jami’an tsaro da mu gwamnati ne jama’a suka dogara da su wajen kare su, kuma mun kasa yin hakan. Amma idan ka duba musabbabin gazawar an kashe jami’an tsaro da dama”
“Har zuwa makonni biyu da suka gabata wani kwamishinan ‘yan sanda ya rasa ransa; wani sifeto ya rasa ransa; an kashe sojoji, jami’ai sun rasa rayukansu a kokarinsu na magance rashin tsaro.
“Rashin tsaro bai shafi jihar Katsina kawai ba, ya shafi kusan kowace jiha a Najeriya da ma wasu makwabtan mu kamar Nijar da Mali su ma suna fama da wannan matsalar.”
Sai dai ya ce: “An samu ci gaba ba kamar da ba, amma ba mu kai inda muke so ba kuma muna rokon Allah daya magance mana matsalar.”
Ya kuma ce Najeriya za ta shawo kan matsalar tabarbarewar tsaro kafin mikawa gwamnati mai zuwa mulki.
A wani lavari kuma na daban.
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani mai kula da gonaki a gonar tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Adebayo Alao-Akala.
Alao-Akala, wanda dan asalin Ogbomoso ne, ya mulki jihar a matsayin gwamna tsakanin shekarun 2007 zuwa 2011.
Ma’aikacin gonar wanda dan asalin Gbongan ne a karamar hukumar Ayedaade a jihar Osun, an yi garkuwa da shi ne a gonar mai suna TDB da ke Jabata a karamar hukumar Surulere a jihar Oyo.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro a ranar Talata cewa ma’aikacin, Christopher Bakare. Wasu ‘yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne sun yi garkuwa da shi da misalin karfe 7 na yammacin ranar Asabar.
Masu garkuwa da mutanen suna kuma neman abiya zunzurutun kudi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar sa.
Wata majiya ta kusa da dangin Alao-Akala kuma dan asalin Ogbomoso, ta tabbatar wa da Jiridar DAILY POST sacen mutumin a ranar Talata.
Ya ce an kai rahoton lamarin zuwa ga ‘yan sanda.
“Mun yi ta kokarin tattaunawa da su duk da cewa an sanar da ‘yan sanda”.
Wata majiyar ta kara da cewa, an sanar da rundunar ‘yan sandan yankin Ogbomoso game da lamarin.
Sai dai duk kokarin da DAILY POST ta yi don jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso ya ci tura domin kiran da aka yi ta wayar salula bai dauka ba, yayin da sakon SMS da aka aika masa shima bai amsa ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.