Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta sanar da fara bincike kan rahotannin da ke cewa wani jirgin yakin ta ya kashe fararen hula bisa “kuskure” a hare-haren da ya yi nufin kai wa kan mayakan Boko Haram a arewacin jihar Yobe.
Mazauna kauyen Buwari da ke gundumar Yunusari a kusa da kan iyaka da Nijar, sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutane 10 ne suka mutu yayin da wasu akalla 19 suka jikkata yayin hare-haren jiragin yakin a ranar Laraba.
Kawo yanzu dai, rundunar sojin saman Najeriya ba ta tabbatar ko musanta adadin wadanda aka kashe ba, sai dai Kakakinta, Edward Gabkwet, ya fitar da sanarwar da ke cewa, tabbas sun samu rahoto kan lamarin kuma sun kaddamar da bincike kan zargin.
Mazauna kauyen na Buwari da dama sun ce jirage masu saukar Ungulu uku sun yi ta shawagi a yankin na su, daga bisani kuma daya daga cikinsu ya bude wuta.