Shugaban kwamitin kar ta kwana na COVID19 Boss Mustapha, ya shaidawa manema labarai cewa Shugaba Buhari ya dauki hukunci kara sati biyun ne domin ganin an dakile cutar kafin kuma a samu damar bude harkokin yau da kullum.
Mustapha wanda shi ne shugaban kwamitin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bada jawabin cigaban da aka samu ga manema labarai game da cutar a ranar Talata.
Wa’adin da aka dauka na sati biyu ya kare a ranar 18 ga watan Mayun da muke, amma shugaban kasa ya kara adadin wasu satin biyun wanda zai kare a ranar 1 ga wata mai kamawa.
Mustapha ya yi kira ga makarantu, wuraren Bauta, kasuwanni da sauran wurare da su yi amfani da wannan lokaci wajen ganin sun kawo matakan kariya daban-daban kamar yadda gwamnati ta shardanta.
Mustapha ya ce “mun san hali fa ake ciki na damuwa da takura amma wannan hukunci da aka na karin sati biyu ya zama dole saboda bada kariya ga al’ummar kasar nan, kuma a sannu komai zai fara tafiya yadda ya kamata”.
“Kuma dole ga kowane dan kasa ya canja halayyarsa game da COVID19 saboda duniya ta canja baki daya”.
A daren ranar Talata hukumar dakile cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa an sake samun sabbin mutane 226 masu dauke da cutar wanda adadinsu ya kai 6, 401 ya zuwa yanzu.
Daga: Abubakar Muhammad Usman