Daga Muhammad Farouk
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari. Masari ya kai wa shugaba Buhari ziyara ne a gidansa dake Daura, inda Masari ya tabbatarwa da shugaban kasa tabbaci akan nasarar da aka fara samu kan kwato daliban ba tare da wani abu ya same su ba.
“muna kan samun ci gaba. Kuma muna da kwarin guiwar samun nasara”. In ji gwamnan ya shaidawa manema labarai bayan ganawa da shugaba Buhari na kusan awa guda.
Gwamnan wanda ya samu rakiyar mataimakinsa, Manir Yakubu ya ce; masu garkuwa da daliban sun tuntube su, kuma tuni aka fara tattaunawa kan yadda za a ‘yanto daliban cikin koshin lafiya zuwa gidajensu.
Gwamna Masari ya tabbatar da cewa; jami’an tsaro tuni suka gano inda aka ajiye daliban. Gwamnan ya ce shugaban kasar ya nuna damuwa da bada goyon baya wajen ganin an ‘yanto daliban, inda ya ce; ya kawo wa shugaban kasar ziyara ne domin yi masa karin bayani kan yunkurin da ake yi wajen ‘yanto daliban.