Gwamnatin Tarayya ta ƙara wa’adin aikin tantancewar ido-da-ido ta masu cin gajiyar shirin nan na tallafa wa matasa, wato N-Power kashi na uku, wato ‘Batch C’.
An ƙara wa’adin ne daga ranar 24 ga Satumba zuwa ranar 30 ga Satumba, 2021.
Shugabannin shirin na N-Power sun bayyana haka ne a wani saƙo da su ka wallafa a shafin su na Facebook a ranar Juma’a.
An bayyana cewa tilas ne duk mai cin moriyar shirin ya je da kan sa a tantance shi kafin a tura shi wurin da zai gudanar da aikin, wato ‘Place of Primary Assignment’ (PPA).
Sanarwar ta ce, “An ƙara wa’adin aikin tantancewar ido-da-ido da ake gudanarwa yanzu ta shirin N-Power ‘Batch C, Stream 1’ zuwa mako ɗaya. Ana sa ran masu cin moriyar shirin za su kammala
tantancewar su ta ido-da-ido daga yanzu zuwa ranar Alhamis, 30 ga Satumba, 2021,” inji sanarwar.
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kafa shirin N-Power ne a cikin watan Yuni, 2016 don magance matsalolin da rashin aiki na matasa ke haifarwa.
Shirin wani ɓangare ne na Shirye-shiryen Inganta Rayuwa na Ƙasa (NSIPs) na gwamnati mai ci yanzu.
Ana gudanar da shirin a Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya a ƙarƙashin Minista Sadiya Umar Farouq.