Gwamnatin Jihar Kaduna ta kulle wuraren sayar da gas ba bisa ka’ida ba guda 87 a cikin jihar bayan gobarar gas din da ta jawo salwantar rayuka biyar a makon da ya gabata.
Shugaban Hukumar kare muhalli na jihar Kaduna, KEPA, Jibrin Lawal, ne ya bayyana haka a Kaduna yayin da ake kwashe abin da ya saura daga wurin da aka yi gobarar.
A cewar Lawal, rufe wuraren na biyo bayan umurnin da Gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i ya yi ne, bayan gobarar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar da raunata mutum hudu.
Ya ce, sun rufe wurare 54 a garin Kaduna, 25 a Zariya da takwas a Kafanchan.
“Zamu ci gaba da rufe wuraren ne saboda har yanzu muna samun korafi daga wadanda suke makwabtaka da wuraren ake sana’ar ne ba bisa ka’ida ba.
Shugaban hukumar ya ce, sana’ar tana da hatsari don haka bai dace yarda a kyale ana yi a kusa da gidajen mutane ba.
Lawal ya ce sun yi aikin ne cikin hadin gwiwa da jami’an Hukumar kula albarkatun man fetur, DPR, Hukumar kula da ingancin kayayyaki na Nijeriya, SON, da sauran hukumomin da abin ya shafa.