Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola ya bayyana cewa gwamnatin tarayya a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kammala aikin titin daya tashi daga Abuja zuwa birnin Algiers na kasar Aljeriya. Fashola ya bayyana hakan a yayin ziyarar gani da ido da ya kai wani sashi na aikin a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba, inda ya ce gwamnati za ta kammala aikin ne cikin shekaru 3 masu zuwa.
A ziyarar Fashola ya leka sashen Abuja-Keffi-Akwanga-Lafia-Makurdi da kuma aikin titin Abuja-Kaduna. Ziyarar na daga cikin ayyukan da aka ware domin taron kwanaki biyu na kwamitin gina sabuwar hanya daga Abuja zuwa Algeria, karo na 70 da aka fara tun a ranar 11 ga watan Nuwamba. “Abinda kwamitin ya fi damuwa da shi, shi ne aikin titin Legas zuwa Algiers, Legas-Ibadan-Oyo- da Jebba-Mokwa-Kaduna-Kano da Abuja-Kano su ne manyan hanyoyin, don haka Mali na yin na ta, Algeria ma haka, Nijar ma haka.” In ji shi.
Ya ci gaba da cewa; hanyar Abuja zuwa Kaduna tagwayen tituna ne dake da tsawon kilomita 375.9 kuma yana da sassa guda uku, sannan ya ce za su kammala shi cikin shekaru uku.
Fashola ya kara da cewa sashen da gwamnati ta bayar da aikinsa ga kamfanin China Harbur Engineering Company Limited shi ne aikin fadada titin Abuja zuwa Keffi tsawon kilomita 5.4 da kuma mayar da hanyar keffi zuwa Akwanga tagwayen tituna.
Ministan ya ci gaba da fadin baya ga gina tituna, za a samar da gadoji da kwalbatoci da kuma hanyoyin matafiyan kasa.
A yayin zagayen, Sakataren kwamitin aikin titin Nijeriya zuwa Algeria, Ayadi Muhammad ya bayyana cewa suma ziyarar ta ba su damar gane ma idanunsu matakin aikin da ake yi. Ayadi ya yaba da ayyukan da ya gane ma idanunsa.
Idan aka kammala wannan aiki, ana sa ran hanyar za ta hada yankunan Afirka guda 37, manyan birane 74 da akalla mutane miliyan 60 daga kasashen Afirka guda 6.
A Nijeriya kawai, titin zai ratsa jihohin Legas, Ibadan, Ilorin, Jeba, Kaduna zuwa Kano inda Nijeriya ta yi iyaka da kasar Nijar. Kasashen da suka dauki nauyin wannan aiki sun hada da Nijeriya, Algeria, Nijar, Mali, Chad da Tunisia.
Tun a shekarar 1966 aka kafa wannan kwamiti domin ta samar da hanyar da ta hada kasashen 6 don karfafa ci gaban tattalin arziki da kuma kawancen cinikayya tsakanin kasashen.