Gwamnatin Tarayya na bukatar a daina amfani da robobi a wani mataki na dakile cutuka da illolin da robobi ke haifarwa a muhalli.
Gwamnati ta ce a maimaikon amfani da robobi a koma amfani da abubuwa masu saurin narkewa.
Mataimakin shugaban hukumar da ke kare muradan masu sayayya Barista Babatunde Irukera ya ce tuni wasu jihohi kamar Kano da Legas suka rungumi wannan tsarin na yadda za su rage amfani da robobi.
Tuni aka fara tattaunawa kan ganin an koma amfani da abubuwan da ba su da illa ga muhalli dalilin ranar ƴancin masu sayayya ta duniya ta 2021, wadda aka yi wa taken “kawo ƙarshen sharar robobi”.
Gwamnatin ta ce za ta shigo da wasu shirye-shirye kan yadda za a rage amfani da robobi a kasar domin rage hadarin da sukan iya haifarwa.