Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumar KASMA ta nuna damuwar ta kan wasu mutane da suke barnatar kebul tare da lalata fitilun kan titi, ta sake jaddada kudirinta na daukar matakin shari’a.
Darakta Janar ta Hukumar Kula da Birane ta Jihar Kano Injiniya Hadiza Ahmad Tukur, ta bayyana damuwarta kan yadda mazauna jihar da masu ababen hawa ke lalata fitilun tituna da wayoyin wutar ba tare da katsewa ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Atiku Ya Fi Cancanta Ya Zama Zabin Yan Najeriya a 2023, Saraki
Shugabar ta bayyana hakan ne a ofishinta a lokacin da take mayar da martani ga wani rahoton barna a Kwanar Dala da kantitin Gwarzo a cikin birnin Kano, wanda ya shafi wasu mutane Haruna Saleh Shuaibu da Alkasim Umar mazauna Rimin Gata.
Injiniya Hadiza Ahmad ta bayyana cewa an mika wadanda ake zargin da laifin lalata fitilun kan titin Gwarzo zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike, inda ta kara da cewa gwamnatin jihar ba ta da hurumin yin barna.
Ta kuma gargadi mutane da su kaurace wa wadannan ayyuka domin gwamnatin jihar za ta gurfanar da duk wanda ke da hannu wajen lalata kayayyakin jama’a.
Shugabar ta ci gaba da bayar da tabbacin gwamnatin jihar ta kuduri aniyar samar da karin ababen more rayuwa da nufin inganta tsaro da ci gaban tattalin arzikin jihar.
A wani labarin kuma, Wata Sabuwa: Al’umma a Zamfara sun nuna takaici kan harin da aka kaiwa Kwamandan Ƴan Bindiga Turji
Wasu mazauna garin Fakai da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara sun bayyana fargabar cewa harin bam da sojoji suka kai a sansanin Turji na iya yin tasiri a kansu.
Mahmud Shinkafi wanda ya yi ikirarin cewa shi ne shugaban kungiyar al’ummar ya shaidawa wakilin DAILY POST a Zamfara cewa sun gaji da gudu don neman tsira.