Ƙasar Saudiyya za ta buɗe sufurin jirage na ƙasa da ƙasa daga ranar Talata, watanni shida kenan bayan zaman ɗar-ɗar kan annobar Korona.
Hukumar ƙasar Saudiyya ta ce daga ranar Talata za a fara barin jam’ian gwamnati da ɗalibai da masu neman lafiya da kuma sojoji su riƙa yin shige da fice.
Waɗanda ba cikakkun ‘yan ƙasar ba za su samu damar shiga ƙasar daga ranar Talata idan har ba a same su da cutar Korona ba, kamar yadda kamfanin diillancin labarai na Saudiyya ya fitar.
Sai dai ta ce “bayan 1 ga watan Janairu shekara mai zuwa” sauran ‘yan ƙasar za su fara fita waje kuma za ta bayyana ainahin lokacin buɗewar cikin Disamba.
Saudiyya ta hana zirga-zirgar jirage tun a watan Maris, wanda hakan ya sa ‘yan ƙasarta da ke Ƙasashen waje kasa dawowa gida.
https://dimokuradiyya.com.ng/covid19-saudiyya-zata-bude-masallatai-a-faɗin-ƙasar/
Gwamnatin ƙasar ta ce za ta sanar da ranar da za ta buɗe ziyarar Umrah a ƙasar.
Saudiyya ta soke ziyarar Umrah clne a watan Maris saboda tsoron yaɗuwar annobar Korona a ƙasarta mai tsarki.
A watan Yuni ƙasar ta rage mutane da za su halarci aikin Hajji 2020 zuwa mutane 10,000 kacal sabanin mutane miliyan biyu da rabi da suka yi hajji shekarar da ta gabata.
Gwamnatin ƙasar ta yi ƙoƙarin hana yaɗuwar cutar da aka samu fiye da mutane 325,000 sun kamu, yayin da fiye da mutum 4,200 suka mutu.
A watan Yuni, gwamnatin ta ɗage dokar da ta saka a ƙasar kan kasuwanci da gidajen sinima da sauran wuraren bukukuwa.