Gwamnatin Jahar Abia ta sanar da mayar da manyan makarantu guda uku, ya zuwa matsayin jami’o’i a jahar, biyo bayan amincewa da Majalisar Dokoki tayi.

KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kakaba wa wasu Al’umomin Sokoto Haraji, Kuma sun bada Wa’adi
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labaru Chief John Okiyi Kalu ya sanyawa hannu aka rarraba wa manema labaru a ƙarshen taron majalisar zartarwa wanda Gwamna Okezie Ikpeazu ya jagoranta a gidan Gwamnatin Jahar na Umuahia a ranar Talata.
Makarantun sun ƙunshi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jahar Abia a Aba, zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jahar Abia, sai kwalejin ilimi ta Jahar Abia zuwa Jami’ar Ilmi ta Jahar Abia, da Kwalejin kula da Lafiya da nazarin mulki ta Jahar Abia zuwa Jami’ar Lafiya da Nazarin Mulki ta Aba.
Gwamnatin ta kuma amince da biyan kuɗi ga Hukumar Kula da bada tallafin karatu ta Jahar Abia domin ta samo tallafin karatu na ƙasashen waje, gami da bayar da tallafin karatu a cikin gida.
Majalisar ta kuma sake yin dubi akan sakin wasu kuɗaɗe da za’a gudanar da manyan ayyuka a gidan Gwamnatin Umuahia.