By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da nadin sabon Alkalin Alkalai, shugaban kotun daukaka kara na shari’a da kuma shugaban kotun daukaka kara na gargajiya.
Gwamna Ahmadu Fintiri ya kaddamar da shugabannin kotunan a ranar Juma’a a birnin Yola.
An kaddamar da Justice Nathan Musa, Usman Girei da Peter Wajilda a matsayin alkalin alkalan Adamawa, Grand Khadi, kotun daukaka kara ta shari’a da kuma shugaban kotun daukaka kara na gargajiya, nan take.
Gwamnan ya bukaci wadanda aka nada dasu yi duk abin da za su iya don inganta tsarin shari’a da tabbatar da adalci a jihar.
“Aikin dake gaban ku ba shi da sauki, duk da haka, ina rokon ku da ku jajirce wajen mayar da bangaren shari’a na gwamnati ya zama na musamman kamar yadda ake tsammani,” in ji Fintiri.
Da yake mayar da martani a madadin wadanda aka nada, Mai shari’a Musa ya tabbatar da cewa za su inganta tsarin doka a jihar tare da kare muradun kowa da kowa.
Babban Lauyan kasar kuma kwamishinan shari’a na kasa, Afraimu Jingi, ya rantsar da sabon alkalin alkalai tare da rantsar da sabon Alkalin, wanda shi kuma ya gudanar da rantsuwar Girei da Wajilda.