By Abbas Yakubu Yaura
Jihar Adamawa ta ce ta tabbatar da mutane 5 wadanda suka kamu da cutar kyandar biri, kuma tana duba wasu mutane 57 da ake zargin sun kamu da cutar.
Ma’aikatar lafiya ta jihar ta ce ta samu dakunan gwaje-gwajen da aka tabbatar da mutane biyar sun kamu da cutar tun daga ranar 12 ga watan Yuni.
KARANTA WANNAN LABARIN: Siyasar Najeriya: Dan Majalisar Wakilai, Shina Peller Ya Fice Daga Jam’iyyar APC
Daraktar Kiwon Lafiyar Jama’a, Dr. Celine La’ori, ta fada a wata hira da manema labarai cewa an samu bullar cutar ta farko a watan Afrilu a babban birnin jihar, Yola.
Ta bayyana cewa, har ya zuwa yau, yaduwar cutar ta barke a kananan hukumomin biyu na Yola ta Arewa da Yola ta Kudu.
La’ori ta ba da tabbacin cewa, domin dakile yaduwar cutar, an kafa cibiyar bayar da agajin gaggawa.
“Wannan ne karon farko da aka samu bullar cutar a jihar, don haka abokan aikinmu ne suka horar da ma’aikata. Mun kuma fara aikin wayar da kan jama’a zuwa yankunan da abin ya shafa,” inji ta.
Ta yi gargadin cewa cutar kyandar biri na da saurin yaduwa kuma ya kamata a ware masu kamuwa da cutar tare da kula da tsaftar su.
La’ori ta ce alamomin kamuwa da cutar sun hada da zazzabi, tare da rashi kuzari kamar murar tsuntsaye.
“Lokacin da kuke da irin wannan rashi kuzari, ku garzaya cibiyar aikin lafiya ta gaggawa don gano ainihin cutar data ke damunku ,” in ji ta.
Kazalika Laori ta koka da karancin ilimin da mutane suke dashi game da kwayar cutar tare da yin kira da a wayar da kan jama’a yadda ya kamata.
Comments 1