Ma’aikatar lafiya ta jihar Akwa Ibom ta koka kan yadda cututtuka masu yaduwa da aka yi watsi da su, ke Kara ta’azzara a kananan hukumomi goma sha daya na jihar.
Wakilin jihar a Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa na duniya na jihar (NTD) kuma Jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya Dr Aniekeme Uwa, ya ce mutane da dama a jihar na rayuwa da cututtukan masu yaduwa Kuma ba a kula da su.
Da yake jawabi a ranar Litinin a garin Uyo domin ganawa da jama’a a ranar yaki da cututtuka masu zafi na duniya (NTD), Uwa wanda kuma shi ne jami’in hulda da jama’a na kungiyar likitocin Najeriya (NMA), ya bayyana cewa NTD na sane da cututtuka kusan 20 dake yaduwa cikin al’uma, inda ya kara da cewa cututtukan sun fi yawa a wurare masu tsananin zafi da kuma yankuna masu zafi na duniya.
Ya bayyana cewa suna da alaƙa da talauci, rashin gidaje, rashin wadataccen ruwan sha, da sauran su, amma ba a ba’a rahoton su, saboda ba sa kashe mutane da sauri kamar sauran cututtuka irin su HIV, da COVID-19 da sauransu.