Gwamnatin jihar Anambra ta bayar da hutun ranar 16 ga watan Nuwamba domin karrama shugabansu na farko a Najeriya Marigayi Dr Nnamdi Azikiwe.
Gwamna Willie Obiano ya ce zai dace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi hakan.
An haifi marigayi Owelle na Onitsha, Dokta Nnamdi Azikiwe, a garin Zungeru na Jihar Neja, a ranar 16 ga Nuwamban shekarar, 1904.
A wata sanarwa da ya fitar yau Litinin a Awka, Obiano ya ce za ta kasance ranar da babu aiki don karrama mutumin da ake kira Zik na Afirka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 51,000 ne zasu amfana da Shirin Inshorar Lafiya
Sanarwar mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a, C Don Adinuba, ta ce: “A ranar Talata, 16 ga watan Nuwamba, 2021, an ayyana ranar da babu aiki a Anambra don karrama Dr Nnamdi Azikiwe, shugaban Najeriya na farko da aka haifa a ranar. Nuwamba 16, 1904.
“Wannan ita ce shekara ta uku a jere da Jihar Anambra ke bikin zagayowar ranar haihuwar mutumin da ya jagoranci Nijeriya ta samu ‘yancin kai a ranar 1 ga Oktoba, 1960, wanda kuma aka fi sani da The Great Zik na Afrika saboda gagarumin hangen nesa da jajircewarsa a Afirka.” Inji sanarwar