Gwamnatin jihar Anambra ta haramtawa mata sanya kananan kaya a makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da makarantun jihar za su ci gaba da gudanar da sabon zaman zangon karatu a ranar Litinin mai zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 19 Ne Suka Hallaka A Wani Mummunan Hatsarin Mota A FCT
Kwamishiniyar Ilimi, Farfesa Ngozi Chuma-Udeh, ta sanar da matakin da gwamnati ta dauka a yayin wani taron tattaunawa da sakatarorin ilimi na makarantun gwamnati da na mishan da aka gudanar a hukumar ilimin bai daya dake Awka ta jihar Anambra a ranar Asabar.
Chuma-Udeh ta yi Allah-wadai da yadda yara mata ke sanya riguna da kananan siket yayin zuwa makarantu.
Ta yi nuni da cewa hakan ba daidai ba ne a da’a kuma Gwamnati ba za ta amince da tsarin da kuma bukata ga yaran ba.
Ta ce yanayin tsayin da aka yarda da shi na rigunan a jihar ya kasance tsayin zuwa gwiwa kuma bai wuce gwiwa ba kamar yadda yake saurin zama salo.
Kwamishiniyar ta bukaci sakatarorin ilimi da su tabbatar da cewa makarantu sun bi umarnin don ceto makomar daliban jihar.
Ta kuma umarci mahalarta taron da su sanya tarbiyya ga yara masu kyau ta yadda za su girma su zama masu nagartattun dabi’u da halaye.
A cewarta, ya kamata dalibai suka kasance suna da wayo, adon kyau, ya samar da yanayi mai kyau kuma kada ya kasance cikin suturar da ba ta dace ba a makaranta, inji ta.
A wani labarin kuma, Zan Jagoranci Najeriya Na Ciyar Da Ita Gaba Da Hikima – Atiku
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi wa matasan Najeriya alkawarin cewa gwamnatinsa za ta zama ta matasa wadanda tabbas sun bambanta a fannonin su daban-daban.
Ya kuma yi alkawarin hada kai da hikima da nagartar matasa domin samar da ingantacciyar mafita da kariya ga Najeriya.