By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP Walid Jibrin a ranar Laraba ya kaddamar da sabon babban asibitin Dambam wanda gwamnatin jihar Bauchi ta gina a kan kudi naira miliyan 330.
Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, Jibrin ya yabawa gwamnan jihar Bala Mohammed bisa nasarorin da ya samu a sassa daban-daban tun hawansa ofis a shekarar 2019.
Ya ce, “Na yi imanin jihar Bauchi ba za ta sake komawa baya ba. Ina so in yi kira ga al’ummar jihar Bauchi da su baiwa gwamna cikakken goyon baya da hadin kai a koda yaushe.
“Na yi imani cewa wannan asibitin da muke kaddamarwa a yau ba wai kawai wurin jinyar marasa lafiya ba ne, cibiyar horar da ma’aikatan jinya da ungozoma. Ina fatan nan gaba za ta zama cibiyar horar da likitoci matasa.
“Ina yaba wa gwamnan jihar Bauchi da ya samar da wannan asibitin domin inganta lafiyar jihar, tare da ganin cewa wannan asibitin zai biya bukatun al’ummar Bauchi ta hanyar magance cututtuka da dama. Kamata ya yi asibitin ya zama abin lura ga sauran asibitoci da dakunan shan magani a fadin kasar nan”.
Gwamnan ya ce an kuma gina wa likitocin da ma’aikatan lafiya gidaje 10 tare da ginin.