By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Bayelsa ta sake yin kira ga matasa a jihar dasu daina gurbata muhalli ta hanyar tace man fetur ba bisa ka’ida ba.
Gwamna Douye Diri ya yi wannan kiran ne a karshen mako, yayin da yake jawabi a wajen taron jana’izar marigayi Dattijo Dick Akpolo a Odi, a karamar hukumar Kolokuma/Opokuma ta jihar.
Sannan ya koka da yadda tace man fetur ba bisa ka’ida ba yake dada matsalar gurbacewar muhalli da tabarbarewar ayyukan ta’addanci da ayyukan hakar mai na kamfanonin mai na kasa da kasa dake aiki a yankin Neja Delta.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, ya bayyana cewa rashin kyawun tace danyen mai shine babban abin dake haifar da gagarumin sauyin yanayi da ake gani a yankin.
Ya kuma bayyana cewa matatar tace man ba bisa ka’ida ba a matsayin ta’addancin muhalli, inda yace matasan dake da hannu a cikin lamarin ba wai suna jefa kansu cikin hatsari ba ne, har ma suna kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kai a kai.
Kazalika yace: “Dole ne matasanmu su yi koyi da salon rayuwar Pa Akpolo. Bai bar muhallinsa da yanayin haihuwarsa su yi masa nauyi ya zama mai butulcewa Allah ba. Ya ɗauki bautar Allah kuma ya ci gaba da aikin soja.
“Tuni kamfanonin mai sun gurbata muhallinmu. Muna fama da wannan wulakanci.Amma yanzu, kuna ƙarawa da shi ta hanyar tacewa mai ba bisa ka’ida ba. Abin da kuke yi ya fi abin da kamfanonin mai ke yi muni, Kuna kashe mu duka a kan kari.”