A ranar Asabar ne gwamnatin jihar Borno ta gudanar da bikin cikar Najeriya shekaru 62 da samun ‘yancin kai, inda aka gudanar da fareti na farko cikin shekaru 12 da fara rikicin Boko Haram.
Gwamna Babagana Zulum ne ya jagoranci bikin da aka gudanar a dandalin Ramat da ke Maiduguri.
KARANTA WANNAN LABARIN: Najeriya Tana Samun Karuwa Duk Da ‘Yan Kalubale — gwamna Abdulrazaq
Ya ce taron ya samu ne bayan dawowar zaman lafiya a jihar.
Zulum, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Usman Kadafur, ya yabawa rundunar soji da sauran jami’an tsaro bisa irin nasarorin da ba a saba samu ba a hare-hare daban-daban kan ‘yan tada kayar bayan.
Gwamnan ya ce nasarorin da aka samu a yakin ta’addancin ya baiwa gwamnatin jihar damar rufe dukkanin sansanonin ‘yan gudun hijira a kananan hukumomin Maiduguri da Jere.
Ya bayyana cewa mafi yawan wadanda suka rasa matsugunan su ne bisa radin kansu sun koma garuruwa da kauyukansu.
Gwamnan ya ce aikin da ke gaban gwamnati shi ne sake gina muhimman ababen more rayuwa da aka lalata a cikin shekaru 12 da aka kwashe ana tada kayar baya a jihar.
“Mun sabunta alkawarinmu na tunkarar kalubalen muhimman ababen more rayuwa da rikicin Boko Haram ya lalata na tsawon shekaru goma.”
“Sannan a binciko hanyoyin samar da guraben ayyukan yi ga dimbin matasan mu da ba su da aikin yi, ta yadda za a rage yawaitar munanan dabi’u a cikin al’umma.”
Ya kara da cewa, “Muna da kwarin gwiwar cewa, tare da dimbin jarin da muka zuba a cikin shekaru uku da suka wuce, wajen fadadawa da karfafa ayyukan sake tsugunar da jama’a, da farfado da ayyukanmu, za mu yi nasara a kan kudurinmu na samar da ribar dimokuradiyya.”
Ya yi alkawarin samar da muhimman ayyuka ga jama’a, don inganta rayuwa da ci gaban tattalin arzikin al’umma.
“A bisa dogaro mai dorewa wajen cimma manufofinmu, ya zama wajibi mu inganta kan samar da ayyukan yi, samar da ilimi, ayyukan samar da lafiya, tsaro, samar da ruwan sha domin amfanin mutane da dabbobi da dai sauransu.”
“Za mu iya yin wadannan ne kawai a cikin yanayin zaman lafiya da tsaro,” in ji Zulum.
Ya kuma yi kira ga al’ummar kasar da su kasance da hadin kai, su zauna lafiya, tare da gujewa duk wata dabi’a da za ta iya jefa al’ummar kasar cikin rudani da rikici yayin da babban zaben 2023 ke gabatowa.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, tawagar jami’an ‘yan sanda sun gudanar da faretin yayin da aka gudanar da wani bikin karrama jami’ai da jami’an Operation Hadin Kai da ke yaki da masu tayar da kayar baya.
An karrama ma’aikatan ne saboda jajircewarsu da sadaukarwar da suka yi a wasu hare-haren da suka kai kan masu tada kayar baya a jihar.NAN
A wani labarin kuma, Matasa Ku Gujewa Bangar Siyasa A Lokacin Zabe – Sarkin Kano
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya roki matasa da su kaucewa siyasar daba da ta uban gida yayin zabe mai zuwa.
Sarkin Kanon ya yi Wanann rokon ne ranar Asabar yayin da ya jagoranci yiwa kasa addu’o’i a Wani bangare na bikin zagayowar ranar samun yancin kai.