Gwamnatin Jihar Borno dake Arewa Maso gabashin kasar nan ta sauya matsuguni wa yan gudun hijira dake zaune a sansanin masu yiwa kasa hidima wato NYSC izuwa wani wuri da ta tanadar a baya-bayan nan.
Kwamishinan Garambawul da kuma Sauya Matsuguni ma yan gudun hijiran Alhaji Mustapha Gubio shi ya bayyana haka a yayin da yake damka sansanin masu yiwa kasa hidimar ga jami’ansa.
Wannan lamari ya sanya yan gudun hijiran nuna farin cikinsu duba da yadda suka shafe tsawon shekara bakwai suna zaune a sansanin, to amma a yanzu haka an maida garin Auyo bayan da gwamnatin ta sake farfado da kauyen.
Yanzu haka gwamnatin ta raba wa Kowane Magidanci naira dubu dari da kuma kayan abinci don rage musu radadin rayuwa da suke ciki.
Da ma dai tun farko gwamnan jihar ta Borno Babagana Zulum ya alkawarta cewa zai rufe sansanin yan gudun hijira uku a karshen watan Mayu, yayin da sauran sansanin yan gudun hijira 24 hudu kuma ya ce za a rufe su ne a karshen shekarar nan.
Kazalika Alhaji Mustapha, ya ce babu tilastawa ga sauya wa yan gudun hijiran matsuguni domin sai daaka basu zabin komawa birnin Maiduguri ko Auno ko kuma inda tun farko ƙauyukan da suka fito.