Gwamnatin Jahar Borno a ranar Laraba ta tabbatar da sace wani Mr Bulama Geidam wani Ma’aikacin Lafiya da yake aiki a Babban Asibitin Gubio, Jahar Borno daga Ƴan Ƙungiyar ISWAP.
Ƴan ISWAP sun kai hari da sanyin safiyar Laraba tare da tafiya da kayan abinci da Man Fetur.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Sanda a Jahar Borno sun cafke soji 2, wasu mutane 3 kan yiwa mai POS fashi da makami
Kwamishinar Lafiya ta Jahar Juliana Bitruce, wadda ta tabbatar da sace shi ga Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a Maiduguri, ta bayyana lamarin a matsayin “abun baƙin ciki da damuwa”.
A cewar ta, wanda suka sace, ya kasance daga cikin waɗanda suke aiki yanda ya kamata, duk da matsalar tsaro a yankin.
“Ma’aikatar zata rubuta tare da sanar da dukkanin Hukumomin tsaro, ciki harda Dakarun Operation Haɗin Kai” inji ta.
Kwamishinar tayi addu’ar samun nasarar sako Jami’in lafiyar cikin nasara.
Amma kuma waɗanda suka gudu domin neman tsira, sun dawo gida, biyo bayan guduwa da ƴan ta’addan suka yi a yankin.
Comments 1