By Abbas Yakubu Yaura
Misis Zuwaira Gambo, kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban jama’a ta Borno, tace gwamnatin jihar ta bada fifiko ga ilimin yara mata.
Gambo ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a Maiduguri ranar Asabar cewa ya dogara ne da fifikon da gwamna Babagana Zulum ya bada umarnin cewa shigar da sabbin manyan makarantun da aka kafa ya zama kashi 60 na ’yan mata da kashi 40 cikin 100 na maza.
Sannan tace gwamnati ta kuma karfafa gwiwar ‘yan matan da suka yi fice musamman daga iyalai marasa galihu da su ci gaba da karatunsu,inda tace ya zuwa yanzu an dauki nauyin karatun ‘yan mata sama da 100 domin karantar harhada magunguna.
Ta kara da cewa, “akwai kuma manufar da aka tsara na cewa cibiyoyin koyon sana’o’in gwamnati zasu yi shiri ga mata da matasa.Har ila yau, mun saka nakasassu a duk cikin gudanar da shirye-shiryenmu. “
Dangane da batun dokar kare hakkin yara da cin zarafin mutane (VAPP), Gambo tace an cimma matsaya da tuntubar juna domin zartar da kudirorin biyu.
Kazalika tace “A makon daya gabata mun dawo daga wani taro kan dokar kare hakkin yara kuma mun riga mun gana da masu ruwa da tsaki kuma mun yi magana a duk wuraren.“Muna jira ne kawai don jin ra’ayin jama’a na karshe, sannan majalisar zata zartar da kudirin neman amincewar Gwamna.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Game da dokar VAPP, mun sami jin ra’ayin jama’a kuma kudirin ya tsallake karatu na biyu a majalisar.inda tace mu dai muna jiran karatu na uku kan dokar”