Gwamnatin Buhari ba zata iya baiwa ASUU fifiko ita kaɗai ba — Inji Garba Shehu
Fadar Shugaban ta caccaki Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya akan yajin aikin.
Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa kan Kafafen Yaɗa Labaru Garba Shehu ya bayyana mamakin yadda ASUU ke ɗora alhaki kan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari akan yarjejeniyar da bai sanyawa hannu ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu-Shettima: CAN na fama da rikicin Ƙwaƙwalwa — MURIC
Shehu ya bayyana yadda aka sanyawa hannu akan yarjejeniya ta Shekarar 2009 ba bisa ƙa’ida ba da Gwamnatin Tarayya.
Da ya bayyana a gidan Talabijin na Channels a Shirin Siyasar mu a yau, Shehu yace Gwamnatnlin Buhari ba zata iya biya buƙatun ba kashi ɗari.
Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na bukatar ta bada fifiko a wasu ɓangarori na Kasar.
A cewar Garba Shehu, Sojoji na bukatar Makamai da zasu yaƙi ƴan ta’adda, a saboda Gwamnati ba zata iya bada fifiko akan ASUU kaɗai ba.
Yace “a matsayin ASUU, Shugaban Ƙasa nada damar da zaiyi kira a madadin ƴan Najeriya, yanzu watanni 6 kenan, ko fiye da haka na yajin aikin ASUU.