Gwamnatin tarayya ta raba buhunan abinci sama da dubu 8 ga marasa galihu a jihar Gombe.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an mika kayayyakin ne ga kungiyoyi da ba su wuce 50 ba, wadanda suka kunshi na addini daban daban, da kuma shugabannin gargajiya.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Ali Pantami, wanda ya wakilci shugaban kasa, Muhammadu Buhari a yayin bayar da tallafin, ya ce kungiyoyin da aka gano wasu mutane ne da aka tabbatar da su, inda ya kara da cewa hakan zai rage musu radadin talaucin da suke fama da shi.
Ya ce, “Kamar yadda kuka sani wannan aikin yana bukatar amana, komai sharrin al’umma, za ku gane akwai nau’in mutane da ake mutuntawa, Rukunin na iya zama ɗaya, biyu ko ma fiye, Mutanen da muka amince da su iyayenmu ne na addini da na sarauta.”
KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Gargadi Masu Amfani Da Kakinta A Shafuka Sada Zumunta
Da yake karin haske, shugaban ya bayyana cewa, wadanda aka tantance don ba da za su cimma manufar karfafar su da ake fata.
Shima da yake nasa jawabin shugaban kungiyar hadin guiwar nakasassu Umar Ali-Goro ya bukaci gwamnatin jihar Gombe da ta tabbatar da raba kayan agajin ga wadanda suka cancanta.
A wani labarin kuma:
EPL: Liverpool Ta Doke Bournemouth Da Ci 9-0
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta daidaita tarihin lashe babbar gasar Premier a ranar Asabar, bayan da ta lallasa Bournemouth da ci 9 da nema.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa was an an buga shi ne a filin wasa na Anfield, kuma wannan wasa ya shiga cikin tarihi musamman irin namijin kokarin da suka yi.