Gamnan Jahar Benue Samuel Ortom yace Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari taki taimaka masa ya kawar da wasu matsaloli na biyan kudade, sabudda kawai yana fadin gaskiya.
Ortom ya bayyana cewa, akwai wadanda suka same shi daga Jami’iyyar APC mai mulki, inda suka ce taimako zai zo ne Jahar Benue idan shi ya koma Jami’iyyar.
Gwamnan yace bashi da ra’ayin sayar da Al’ummar sa, kamar yadda wasu Gwamnoni suke yi a yanzu, inda yace zai cigaba da jajircewa akan su.
Ortom ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta Daily Post, akan yadda ya samu nasarar shimfida ayyuka masu yawa da kudin da Gwamnatin sa ke samu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 7 sun mutu, yayin da Mota ta afka Kogin Niger
A cewar Gwamnan “Ina godewa Allah, duk da anyi mani wulakanci, an bata mani suna da sauran abubuwa. Amma ni ina son kasar nan ta samu cigaba.
“Nayi imani da kasa ta Nigeria, wannan ne ya sanya nake dauke da kalar Nigeria, kuma kalar manyan kabilu na Kasa a Benue kamar su; Tiv, da Idoma, da Egede.
“To nayi Imani akan Nigeria daya. Hadin kai muke so kuma bama son rabuwa. Karfin mu shine hadin kai. Kuma nayi Imani mutanen mu zasu kasance akan haka.
“Wani abu dana rike shine nayi rantsuwar kama aiki da littafina na Bible, kamar yadda Shugaban Kasa yayi rantsuwar kama aiki da Al-kur’ani, to abinda nayi imani shine fadin gaskiya a kowane lokaci.
“A kowane lokaci dole zamu kare kundin tsarin Mulkin Nigeria. Wannan shine na tsaya akanshi, kuma zamu cigaba da yaki akan dai-dai to, da gaskiya da adalci.
“Gwamnatin Tarayya taki taimaka mani wajen tabbatar da biyan kudaden ariyas na Fansho da garatuti Wanda na gada, ba laifi na bane. Aper Aku yana da alhakin biyan kudaden ariyas na Fansho da garatuti, Akume yana da hakan, Adasu na dashi, Suswan yana dashi, Na gaji biyan Naira biliyan 70 na kudaden ariyas na Fansho da garatuti da zan biya, don haka wannan sabon abu bane.
“Gwamnatin Tarayya ta bani Biliyan 28 amma bata isheni ba. An ba wasu Karin kudade, amma sabudda ina fadin gaskiya, sun ki bani kudi.
Gwamna Ortom wanda ya lashe kujerar Gwamna a karkashin inuwar Jami’iyyar APC, ya bar Jami’iyyar gabanin Babban zabe na Shekarar 2019, inda ya samu nasarar lashe wa’adi na biyu a karkashin Jami’iyyar PDP.