By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin Cross River ta caccaki rahotannin kafafen yada labarai da ke cewa ta kasa biyan albashin ma’aikata da kuma kyauta ga ‘yan fansho a jihar.
DUBA WANNAN LABARIN: Jihar Colorado A Amurka Ta Sanya Hannu Kan Dokar Baiwa Mata Damar Zubar Da Ciki
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar (HOS), Mista Timothy Akwaji a ranar Talata a Calabar.
Akwaji ya ce rahotannin na batanci ne, ba gaskiya ba ne, kuma an hada su ne domin bata sunan Gwamna Ben Ayade.
“Ko da a fuskanci kalubalen shigo da kudaden shiga, gwamnatin jihar ta na sanya kari a kan biyan albashi da fansho.
“Ba za a iya cece-kuce ba cewa ko da a fuskanci kalubalen kudaden shiga, hadi da kashe basussukan da suka wuce, gwamnatin Ayade ta sanya a addinance ta biya albashi da fansho ga kowa da kowa.
“Duk da haka, duk wani mutum ko gungun mutanen da suka yi ikirarin cewa suna bin bashin albashi da fansho to su tura irin wannan ga hukumar ta HOS don bincike da kuma daukar mataki.
“Gwamnatin Jiha ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta wadanda ke kitsa wannan mugunyar farfaganda mai rahusa da nufin haifar da rashin jituwa a jihar,” in ji shi.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da mai da hankali wajen ganin ta magance matsalolin ma’aikata da manyan mutanen jihar. (NAN)