By Ishaq Dabai
A ranar Talatar data gabata ne gwamnatin jihar Enugu ta dakatar da Igwe Anthony Okorie,mai rike da Sarautar Gargajiya ta Jama’ar Amechi Awkunanaw mai cin gashin kanta a karamar hukumar Enugu ta Kudu.
Dakatarwar tana kunshe ne a cikin wasikar da kwamishinan masarautu, Dakta Charles Egumgbe ya mika wa uban sarautar.Gwamnati ta dora alhakin matakin da janye ma’aikatan Ofishin daga Okorie kan “rikicin dake ci gaba da faruwa a cikin al’umma”.
Ya bayyana cewa rikicin ya bijire wa duk kokarin da aka yi na magance shi.sai dai Basaraken gargajiyar yace jami’in ‘yan sanda na yankin kuma shugaban ma’aikatar hidimar jaha mai kula da al’umma a duk al’amuran tsaro da tarurrukan su da shuwagabanni ba su taɓa yin korafin rashin tsaro da rikici ba.
“Babu wani abin da ya faru na rashin tsaro ko kadan a cikin Amechi.“Amma dakatarwar matsayi ne da aka kaddara.An riga an rubuta wasiƙar dakatarwa kafin ya gayyace ni don jin tawa.
Kazalika Ya yi kira ga Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi daya kafa kwamitin da zai binciki batun kwace filaye a cikin garin Amechi kuma “kar a dakatar da Igwe din mu.
Comments 2