Kungiyar matasan Fulani ta Jonde Jam ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba matsalolin makiyayan jahar Filato da suka shafi ilimi da kiwo don magance su.
Shugaban kungyar, Alhaji Saidu Maikano, ya ce, gwamnatin jihar Filato ba ta cika alkawuran da ta yi wa makiyayan jihar ba, a lokacin da take neman zabe ba. Kamar yadda VOA Hausa suka tabbatar.
A bangare guda kuwa, Abdulkarim Bayero da ke zama tsohon shugaban matasan kungiyar Miyetti Allah ta kasa ya ce, makiyayan jihar Filato sun amfana daga wannan gwamnati.
Sakataren jami’iyyar APC a jihar Filato, Bashir Musa Sati ya ce, gwamnati ta gyara makarantun Fulani makiyaya.
Shugaban kwamitin sasanta makiyaya da manoma, kuma shugaban CAN na jihohin Arewacin Nijeriya, Rabaran Yakubu Pam, ya shawarci duk mai wata matsala da ya bi hanyar da ta dace wajen isar da kokensa wa hukumomi.