Idan za’a iya tunawa cewa gwamnatin jihar Filato ta fitar da sanarwar manema labarai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba shekarar 2021, inda ta ce, za ta yi karin haske kan zanga -zangar da daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar dake garin Barkin Ladi suka yi, wanda ya haifar da toshe babbar hanyar shiga jihar daga harabar makarantar da Jos.
A cikin bayanin, an ba da dalilan da suka haifar da zanga -zangar ɗaliban, wanda hukumar Masana’antar ta ce, ta dage jarabawar Kwalejin da aka shirya fara Gudanarwa a ranar litinin din 20 ga Satumban shekarar 2021.
Hakan ya sa jim kadan bayan mataimakin gwamnan jihar Farfesa Sonni Gwanle Tyoden, ya gana da kungiyoyin kwadago, masu kula da makarantar, da wakilan kungiyar dalibai don warware matsalar, Wanda daga bisani akafitar da sanarwar manema labarai Wanda babu rahoton mutuwa a sakamakon zanga -zangar, baya ga wasu ɗaliban da aka ruwaito sun ji rauni, kuma aka kai su wani asibiti domin duba lafiyar su.
Sai dai daga baya Gwamnati ta yi nadamar samun labarin bakin ciki daga Jami’an Rundunar Yan sanda, na mutuwar daya daga cikin daliban da aka ce harsashi ne ya same shi, kuma aka kai shi asibiti don yi masa magani amma ya rugamu gidan gaskiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Boren Yan Okada a Legas ya lakume ran wani jami’in Dan sanda
Kazalika hakan yasa Gwamnatin jihar ta bada umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa, domin binciko musabbabin mutuwar dalibin.
Yayin da take jajantawa iyalan dalibin da ya rasa ransa, Gwamnatin jihar ta Filato, ta tabbatar da cewa, ba za ta kyale duk wanda aka samu da laifi a mutuwar dalibin ba.
A halin yanzu da mataimakin gwamnan jihar, ya nada wata tawagar Gwamnati Wanda Kuma ya umarce su, da su ziyarci iyalan dalibin da ya rasu, donmin jajantamu su kan rashin da su kayi.