By Ishaq Dabai
Gwamnatin jihar Gombe ta amince da sama da naira biliyan daya don biyan kudaden takwaran aikin UBEC, diyyar filaye da inganta asibitoci biyu.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar Mista Julius Ishaya ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar.Ishaya yace an amince da jimlar kudi Naira miliyan 715 don biyan kashi 50 na kudin UBEC na shekarar 2021 don samun damar sauran kashi 50 na UBEC.
Hakanan an amince da jimlar Naira miliyan 117 don haɓaka asibitin Cottage da Cibiyar Kiwon Lafiya matakin Farko a Kuri dake ƙaramar hukumar Yamaltu da Deba.
Sannan Yace matakin inganta cibiyoyin kiwon lafiya guda biyu ya biyo bayan mummunan halin da suke ciki, a cewarsa, an sami barkewar cutar a mai da gudawa a yankin kuma cibiyoyin kiwon lafiya biyu sun wuce gona da iri, don haka akwai bukatar ingantasu
Alhaji Usman Jafun, Kwamishinan filaye da safiyo, yace majalisar ta amince da Naira miliyan 177 don biyan diyyar filayen da aka ware wa Jami’ar Tarayya Kashere (FUK) da kwakejin fasaha ta Kaltungo da kuma Golf Coursein Gombe.