Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya amince da daukar kwararrun ma’aikatan lafiya 440 domin magance karancin ma’aikata a fannin lafiya na jihar.
Dokta James Madi, Shugaban Kwamitin Kula da Ma’aikatan Lafiya ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar manema labarai da ya sanya wa hannu yau Lahadi a Gombe.
Ya ce an yanke shawarar daukar ma’aikatan lafiyar ne sakamakon karancin kwararrun ma’aikata a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a jihar.’
“Muna bukatar mu magance hakan, musamman a matakin kiwon lafiya na farko, wanda shine tushen tsarin kiwon lafiya,” in ji shi.
A cewarsa, masu nema dole ne su kasance masu rijista kuma suna da lasisin ungozoma, da shaidar Ma’aikacin Lafiyar Jama’a (CHEW) tare da lasisin aiki mai ƙima.
Ya kara da cewa masu bukata su mika takardunsu ga hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar.
Madi ya kuma ce ya kamata masu aikin lafiya na sa kai da suka cancanta suma su nema.